Tawagar ECOWAS a zaben Najeriya | Labarai | DW | 02.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tawagar ECOWAS a zaben Najeriya

Kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS tace zata aike da wakilanta domin sa ido a babban zabe na taraiyar Najeriya,karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar gambia dauda Jawara.

Kakakin kungiyar Abdelfatau Musah yace tawagar zata hada da membobin majalisar dattawan kungiyar su 7 tare da yan majalisar gudanarwarta da kuma jakadun kasashen kungiyar a Najeriya.

Zata kuma hada da kwarraru kann harkokin zabe da wakilan kungiyoyi dabam dabam da zasu sa ido akan zabena dukkan shiyoyi 6 na fadin kasar ta Najeriya.

Kungiyar ta ECOWAS tace ta yanke shawarar aikewa da tawagar ce biyowa bayan wata ziyarar bincike da wakilanta suka kai ne kasar inda suka gana da shugaban OBJ da Atiku da kuma membobin majalisa.