Tawagar ƙasashen larabawa a Isra´ila | Labarai | DW | 25.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tawagar ƙasashen larabawa a Isra´ila

Tawagar ƙungiyar ƙasashen larabawa, ta gana da hukumomin Isra´ila, a game da batun farfaɗo da shirin zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya.

Wannan tawaga da ta ƙunshi ministocin harakokin wajen Masar da na Jordan, ta gana da shugaban ƙasa Shimon Perez, da kuma shugaban jam´iyar adawa Benyamin Nitenyau.

A lokacin ganawar ta, da ministar harakokin wajen Isra´ila Zipi Livni tawagar, tawagar larabawa ta shawarci Isra´ila ta yi anfani da taswira zaman lahia da ƙasashen su ka gabatar mata,a lokacin da su shirya a ƙasar Saudi Arabia. Wannan taswira ta tanadi cewar, Irsra´ial ta fita daga yankuna Palestinawa da ta mamaye, muddun ta na buƙatar ƙulla mu´amila tare da ƙasashen larabawa.

Zipi Livni, ta bayyana gamsuwa da wannan tantanawa.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Amurika, ta yaba wannan tantanawa to saidai ta bayyana bada fifiko ga tantanwar gwa- da gwa, tsakanin Palestinawa da Isra´ilawa, a maimakon shiga tsakanin ƙasashen larabawa.