Tauye yancin dan Adan a Nigeria | Labarai | DW | 25.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tauye yancin dan Adan a Nigeria

ƙngiyar kare haƙƙin bil Adama ta Human Rights Watch, ta buƙaci gwamnatin tarayyar Nigeria, ta yi gyara a kan manufar dake nuna banbanci a tsakanin waɗanda suke yan jiha da kuma waɗanda ba yan asalin jiha ba. A wani rahoto da ta fitar ƙungiyar, ta baiyana damuwa da cewa aƙidar nuna wariya ta kasancewa ɗan Jiha, da wanda ba ɗan asalin jiha ba, na maida miliyoyin yan Nigeria dake zaune a sassan jihohin ƙasar tamkar bare a ƙasar su ta haihuwa. ƙungiyar ta Human Rights Watch, ta ce wannan akida ya saɓawa kundin tsarin mulkin Nigeria da kuma dokokin kare haƙƙin bil Adama na ƙasa da ƙasa. Daraktan kungiyar kare haƙƙin bil Adaman ta Human Rights Watch, Peter Takirambude, ya baiyana rarrabewar da ake yi tsakanin ɗan asalin jiha da wanda ba ɗan jiha ba, da cewa shi ne yake haddasa rigingimun addini dana ƙabilanci a Nigeria. Yana mai cewa Gwamnatocin jihohi dana ƙananan hukumomi sun kafa dokoki masu sarƙaƙiya wanɗanda ke nuna wariya ga waɗanda ba yan jiha ba, inda ake hana musu cin gajiyar abubuwan more buƙatun rayuwa dana tattalin arziki. Jamaá da dama na baiyana raáyi cewa, batun ɗan jiha da wanda ba ɗan jiha ba, shi ne babban ƙalubale a zamantakewar alúmar Nigeriar mai ƙabilu fiye da 250.