Tattauwa tsakanin Obasanjo da Paul Biya | Labarai | DW | 11.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattauwa tsakanin Obasanjo da Paul Biya

Shugabannin kasashen Kamaru da Najeriya zasu gana ranar litinin a kasar Amurka idan Allah ya kai mu,a wani yunkuri na sasanta rikicin yankin Bakassi mai arzikin man fetur.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan shi zai karbi bakuncin wannan ganawa tsakanin shugaba Obasanjo na Najeriya da kuma takwaransa na Kamaru Paul Biya.

Wannan rikici tsakanin makwabtan biyu,ya taallake ne kan mallakar yankin Bakassi mai murabbain kilomita dubu wanda keda albarkatun mai,da kuma su.

A watan oktoba na 2002 kotun kasa da kasa dake Hague ta yanke hukuncin cewa yankin mallakar kasar Kamaru ne,amma akwai dubban yan Najeriya da suke zaune a yankin,haka kuma gwamnatin Obasanjo ta gagara cimma waadi da dama na janye dakarunta daga yankin.

Jamian gwamnati sunce a ganawar ta ranar litinin zaa tattauna batun yadda zaayi da dinbin yan najeriya mazauna yankin na Bakassi.