Tattaunawar sulhu ta ci tira a Kwango
December 24, 2016A ranar 20 ga watan nan na Disamba ne dai Shugaba Kabila ya cika wa'adinsa na biyu da ke zama na karashe ya mika mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, amma yinsa kememe ya bar mulkin ya jawo zanga-zanga da ta yi sanadi na rayukan mutane 40 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta nunar.
Shugabannin Cocin Katolika masu fada a ji a kasar ta Kwango sun jagoranci zaman sulhu a tsakanin 'yan siyasar kasar da gabatar da wani daftari da zai sanya Shugaba Kabila ya sauka daga mulki a shekara mai zuwa, a yi sabon zabe. Sai dai fitar mahalarta tattaunawar tun da misalin karfe 05:30 na safiya agogon kasar ba tare da sake komawa ba da misalin sha daya da aka tsara, ya sanya an sake komawa ruwa, fargabar fadawa rikici da kasar ta sha gani a baya ta dawo sabuwa.
Abin da ake gani dai kawo yanzu manyan 'yan siyasar kasar ke zagon kasa ga kokarin da cocin ke yi a fadar wani fada da bai so a bayyana sunansa ba.