1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar sulhu kan yankin Darfur

October 7, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9A

Daya daga cikin madugan yan tawaye na Sudan yace ba zai halarci taron sulhun kasar Libya da aka shirya yi kann Darfur ba. Mr Khalil Ibrahim ya kara da cewa, matukar taron ya gayyaci fiye da kungiyyar yan tawaye biyu, to babu shakka ba zai halarci taron ba.Haka kuma shugaban kungiyyar yan tawayen ta Justice and Equality Movement, ya soki lamirin masu shiga tsakanin da cewa suna tafiyar hawainiya. A tattaunawa data gabata a baya dai kungiyyar yan tawaye daya ce daga cikin uku ta rattaba hannu kann yarjejeniyar sulhun da aka cimma.Kungiyyar Au da Mdd ne dai ke a matsayin masu shiga tsakanin , don ganin cewa an kawo karshen rikicin yankin na Darfur. A wani lokaci ne a cikin wannan wata ake sa ran gudanar da taron sulhun na gaba kann Darfur din a kasar Libya