Tattaunawar sulhu a Uganda ta dau hanya | Labarai | DW | 01.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawar sulhu a Uganda ta dau hanya

Wakilan kungiyyar yan tawaye ta LRA a Uganda ta isa birnin Kampala, don saduwa da shugaba Yoweri Museveni.Wannan dai shine karo na farko da bangarorin biyu zasu gana da juna, a tsawon wani dogon lokaci . Akwai hasashen cewa tattaunawar ka iya taimakawa, wajen kawo karshen yakin basasar kasar na tsawon kusan shekaru 20 da suka wuce.Tuni dai kotun kasa da kasa dake tuhumar wadanda suka aikata miyagun laifuka ta bayar da umarnin cafke mutane 5 na kungiyyar yan tawayen ta LRA.Rahotanni dai sun rawaito shugaba Museveni na cewa,matukar kungiyyar ta LRA ta yarda da tayin sulhun da gwamnati ta gabatar mata, to babu wanda za´a mika hannun kotun ta kasa da kasa. Da yawa dai daga cikin yan tawayen na LRA na boye ne a surkukin daji dake a gabashin kasar Kongo