1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cimma yarjejeniya kan nukiliyar Iran

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 5, 2015

Kasashe shida masu karfin fada aji a duniya sun kai matakin dab da na karshe wajen cimma yarjejeniya ko kuma akasin haka a tattaunawar da suke yi da Iran dangane da batun makamashin nukiliyarta.

https://p.dw.com/p/1Ft7H
Tattaunawar nukiliyar Iran
Tattaunawar nukiliyar IranHoto: Reuters/C. Barria

Shugabar sashen hulda da kasashen ketare ta kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ce ta bayyana hakan bayan da ta isa Vienna domin shugabantar zaman teburin tattaunawar da ake yi tsakanin ministocin kasashen ketare na Iran da kuma na kasashen Birtaniya da Amirka da Rasha da Faransa da China da kuma Jamus. Mogherini ta ce in har za a cimma yarjejeniyar da za ta takawa Iran birki wajen mallakar makaman kare dangi kamar yadda suke zarginta da kokarin yi to yanzu ne. An dai kwashe tsahon shekaru ana ta takaddama kan batun nukiliyar inda a tsahon shekaru biyu aka yi ta kai gwauro ana kai mari domin cimma matsaya guda. Kasashen shida masu karfin fada aji a duniya dai sun bukaci Iran da ta takaita shirin nukiliyar nata yayin da su kuma a nasu bangaren za su cire mata takunkumin karya tattalin arzikin da suka kakaba mata.