Tattaunawar hadin guiwa | Siyasa | DW | 17.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tattaunawar hadin guiwa

An shiga tattaunawar hadin guiwa tsakanin CDU/CSU da SPD

Daya daga cikin muhimman batutuwan da suke neman cimma daidaituwa kansu domin kafa wata sabuwar gwamnati karkashin Agela Merkel kafin nan da karshen watan nuwamba mai zuwa shi ne gyara ga kasafin kudin gwamnati. Domin kuwa wajibi ne a yi tsumulmular abin da ya kai Euro miliyan dubu 14 da rara a shekarar kudi mai kamawa ta 2006 ta yadda Jamus zata cika sharuddan daidaita kasafin kudin kasa na kungiyar tarayyar Turai a shekara ta 2007. Dukkan sassan biyu dai sun dace akan cewar wajibi ne gwamnati tayi tsumulmular kudi, amma akwai banbance-banbance tsakaninsu a game da yawan abin da za a yi tsumulmularsu da kuma hanyoyin da za a bi a cimma wannan manufa. Su ‚yan Christian Union na bukatar ganin an nemo karin rancen kudi domin cike gibin da ake fama da shi a kasafin kudin wannan shekarar, wanda kuma ya samu sakamakon yawan abin da gwamnati ke kashewa akan manufofinta na garambawul ga kasuwar kodago da kuma gibin kudaden fansho. Wannan maganar ka iya haddasa mummunan sabani a zauren shawarwarin hadin guiwar tsakanin ‚yan Christian Union da Social Democrats a cewar Volker Kauder, sakatare-janar na jam’iyyar CDU:

Ko shakka babu za a tattauna maganar rancen domin cike gibin kasafin kudin ko da yake ‚yan Social Democrats ba su tattare da wannan ra’ayi. Za a mayar da hankali sosai akan wannan batu a zauren tattaunawar.

Da farko dai wajibi ne dukkan jam’iyyun hadin guiwar sun cimma daidaituwa akan wata manufa dangane da maganar ta tsumulmular kudi ta yadda za a iya daidaita yawan abin da gwamnati ke kashewa da abin dake kwarara zuwa baitul-malinta. Domin kuwa Jamus ta dade tana keta sharuddan yarjejeniyar Maastricht, kuma muddin aka ci gaba akan haka tilas ne a ci ta tara a shekara ta 2007. Wannan shi ne dalilin da ya sanya Peer Steinbrück da ake fatan nadawa mukamin ministan kudi nan gaba yake dagewa akan maganar ta tsumulmular kudi, inda yake cewar:

Wajibi ne mu yi sara tare da duban bakin gatari ta yadda zamu cimma ka’idar nan ta gibin kasafin kudi na kashi 3% da aka kayyade a yarjejeniyar Maastricht nan da shekara ta 2007. Kuma wannan maganar ta shafi miliyoyi dubbai ne na Euro.

Ayar tambayar dake akwai dai ita ce, shin wace hanya ce za a bi domin tsumulmular wadannan makudan kudi ba tare da mutane sun ji radadin lamarin ba? Matsalolin dai na da yawa kama daga guraben ayyukan yi ga jama’a da damar dake akwai ta tsumulmular kudi da neman sabbin hanyoyin kudaden shiga domin cike gibin da zai samu ga kasafin kudin gwamnati, amma duk da haka dukkan sassan na tattare da kwarin guiwar cimma wata manufa mai sassaucin da zata gamsar da dukkan bangarorin biyu.