1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar Darfur ta gamu da kiki kaka

January 4, 2006
https://p.dw.com/p/BvDn

Darfur/Abuja

Tattaunawar sasanta rikicin Darfur tsakanin bangarorin dake yaki da junansu game da raba iko ta taazzara ,abinda ya kawo nakasu ga kokarin lalubo hanyar samarda masalaha a rikicin baki daya wanda akayi shekaru uku anayi.

Tattaunawar wadda ke gudana a Abuja babban birninNajeriya tsakanin kungiyoyin tawaye na Darfur din biyu da gwamnatin Sudan ta kai zagaye na bakwai amma dai da dukkannin bangarorin suka amince a ajiye wasu batutuwan raba iko biyu.

Sai dai a yanzu shugaban kungiyar yantawaye ta Justice and Equality Movement Ahmad Tugod yace babu ta yadda za asami fahintar juna a sauran fannoni matukar ba a kammala da maganar raba iko ba.