Tattaunawar cimma sulhu a tsakanin Iran da Russia | Labarai | DW | 21.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawar cimma sulhu a tsakanin Iran da Russia

A wani lokaci ne a yau talata wakilan kasashen Iran da Russia zasu koma zagaye na biyu a tattaunawar da suka fara don nemo bakin zaren warware rikicin nukiliyar kasar ta Iran.

Jami´an kasashen biyu dai zasu tattauna ne a game da yarda ko akasin haka a game da shawarar da kasar Russia ta basu na sarrafa sanadarin Uranium din na Iran a cikin kasar ta Russia.

Rahotanni dai sun nunar da cewa a zama na farko taron ya tashi ba tare da cimma wata matsaya guda ba.

Da yawa dai daga cikin kasashen duniya na kallon wannan tattaunawa a matsayin wata kafa ta kwantar da wannan rikici dake ci gaba da daukar hankalin kasashen yamma.

Kafin dai daukar wannan mataki, Amurka tace kamata yayi a kakabawa kasar ta Iran takunkumi, wanda a hannu daya kuma wasu kasashen yamma suka ce kamata yayi a warware rikicin ta hanyar sulhu.