TATTAUNAWAR BUSH DA ANAN | Siyasa | DW | 04.02.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TATTAUNAWAR BUSH DA ANAN

Sakataren Mdd Kofi Anan ya tabbatar da cewa nan bada dadewa ba zai tura Jamian majalisar dinkin duniya izuwa kasar iraqi don taimakawa wajen mika ragamar mulkin kasar daga hannun sojojin taron dangi izuwa hannun yan kasar.
Kofi anan ya nunar da cewa duk da yake yanzu haka akwai sabani a tsakanin kabilun kasar dangane da yadda gwamnatin rikon kwaryar kasar ta wakilai daga bangarori daban daban zatakasance,amma inji Anan jamian sa zasu tabbatar da cewa komai ya dai daita kafin ranar 30 ga watan yuni na wan nan shekara da muke ciki,wanda shine wa,adin da Kofi Anan da shugaba Bush na Amurka suka amince dashi na mika mulkin hannun yan kasar ta iraqi.
Babban sakataren mdd dai ya fadi wadan nan kalaman ne jim kadan bayan ya gana ido da ido da Shugaba Bush na Amurka jiya talata a fadar sa dake white House.
Kofi Anan yaci gaba da cewa tuni gwamnatin rikon kwarya da Amurka ta nada a kasar ta iraqi ta amince da karbar matakin data yanke dangane da sulhunta rikice rikicen gudanar da zaben na mikawa yan kasar milkin su a hannun su.
Bugu da kari Anan ya tabbatar da cewa jamian mdd da zai tura izuwa kasar ta iraqi nada hurumin waiwaye wanda hausawa kance adon tafiya dangane da duba yiwuwar gudanar da zabe ko kuma kasasin hakan.
To amma kuma duk da irin halin dar dar da yakin iraqi ya haifar ga yan kasar da kuma ita kanta kasar,a hannu daya kuma da rashin gamsassun bayanai da Amurka da Biritaniya suka gaza nunawa na dalilin yin yakin, Kofi annan yaki yace komai dangane da kalubalantar kasashen na gudanar da wan nan yaki,a maimakon hakan ma cewa yayi zai tsaya yaga sakamakon rahoton kwamitin bincike da Bush zai kafa dangane da hakan kafin yace uffan.
Majalisar dai ta dinkin duniya a baya ta janye jamian nata daga kasar ta iraqi ne a bayan da aka kaiwa babban ofishin ta dake birnin Bagadaza hari na kunar bakin wake,wanda hakan yayi sular mutuwar mutane da daman gaske ciki kuwa har da babban jakadan majalisar a kasar ta iraqi.
Shirin dai gwamnatin na Bush game da mika mulki hannun yan kasar ta iraqi ya samu akasi ne bayan da shugaban shi,awa na iraqi Ayatolla Ali al Sistani yayi kiran da,a gudanar da zabe na kai tsaye a cikin kasar ba tare da wani bata lokaci ba.
A baya dai gwamnatin ta shugaba Bush tayi niyyar mika mulkin ne hannun yan kasar ta iraqi a ranar sha biyar ga watan nuwanba na wannan shekara da muke ciki,amma yanzu kuma sakamakon kiraye kiraye da kabilun kasar suke na muradin tafiyar da mulkin kasar su da kansu ya haifar dole kasar ta Amurka ta yarda ta canja wan nan mataki data dauka a baya.
Jim kadan kuwa bayan tattaunawar tasu a white House,shugaba Bush ya fada cewa dashi da Kofi anan sun tattauna batutuwa ne da suka shafi ceto rayukan mutanen kasar iraqi ta hanyar gudanar da zabe na mika musu mulkin su a hannun su a hannu daya kuma da abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya.
Bisa hakan ne kuwa Shugaban na Amurka yace yana maraba yayi aiki kafada da kafada da Kofi anan din don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu game da wan nan buri da aka sa a gaba.