1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar Abbas da Mr Olmert

Ibrahim SaniDecember 27, 2007
https://p.dw.com/p/Cgun

Faraministan Israela Ehud Olmert na ganawa da takwaransa na Falasɗinawa Mahmud Abbas, a birnin Jerusselem. Shugabannin zasu mayar da hankali ne kan samo bakin zaren warware rikicin dake tsakanin yankunan biyu ne. Wakilin Falasɗinawa a tattaunawar sulhu, Mr Said Erekat ya ce batun mamaye da Israela keyi a yankunan Falasɗinawa, abune da zai ɗauki hankali a lokacin tattaunawar.Rahotanni dai sun ce, Mr Abbas zai amfani da wannan dama, wajen buƙatar dasa aya ga wannan mataki na Israela. Matakin na Israela a cewar rahotanni, abune dake mayar da hannun agogo baya,dangane da cimma sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu. Tattaunawar ta yau ta kasance irinta ta farko a tsakanin shugabannin, a tun bayan taron suolhun Annapolis da Amirka ta ɗauki nauyin shiryawa