1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TATTAUNAWA KAN MAKOMAR IRAQI.

Yahaya Ahmed.December 3, 2003
https://p.dw.com/p/BvnG
Duk kwararrun masanan da suka halarci taron da aka yi a Brookings-Institut a kan batun Iraqin a birnin Washington, sun taba kai ziyara a kasar don gano wa idanunsu yadda ababa ke wakana bayan hambarad da gwamnatin Saddam Hussein da dakarun Amirkan suka yi. An dai sami bambance-bambancen ra'ayoyi a kan fa'ida ko kuma cikas din manufofin afka wa Iraqin da yaki. Game da yakin sunkurun da ake ta gudanarwa a halin yanzu a kasar dai, wasu masana kan harkokin tsaro, kamarsu Michael O'Hanlon na, sun yi imanin cewa, nan ba da dadewa ba, sojojin mamaye na Amirkan sa su fatattaki duk `yan sari ka noken da a halin yanzu ke ta kai musu hare-hare. O'Hanlon, wanda asalinsa dan kasar Amirkan ne, wanda kuma bisa dukkan alamu yake goyon bayan afka wa Iraqin da aka yi, ya bayyana cewa:-

"Kawo yanzu dai, mun kame ko kuma mun kashe `yan tsagerun Iraqin kusan dubu 5 zuwa dubu 10. Babu shakka, a wasu lokutan mun harbe wasu wadanda ba ruwansu da wannan rikicin, ko kuma mun kame mutane da dama, wadanda daga baya muka lura cewa ba su da wani laifi, muka kuma sake su. Gaba daya dai, mun kashe masu gwagwarmaya da mu da yawa fiye da wadanda ke ta fafatawa da mu a halin yannzu. Kazalika kuma, ina zaton, kamar yadda Janar Abizaid ya kiyasta, yawansu bai wuce dubu 5 ba."

Mafi yawan `yan sari ka noken Iraqin dai, sun dau makamai ne saboda rashin wata hanyar samun kudi. Ko wane sojan Amirka daya da suka kashe, ana ba su dola dari biyu da 50. Ba imanin da suka yi da wata manufa ne ke sanya su shiga yakin sunkurun ba, a daura da yakin Vietnam, inda `yan wannan kasar suka sadaukad da ransu saboda rungumar da suka yi da akidar kwaminisanci.

A bangaren hulda da fararen hular kasar Iraqin kuwa, wasu masanan na nuna shakkunsu ga ikirarin da Amirkan ke yi na samun ci gaba. Kenneth Pollock na cibiyar nan ta Saban, mai nazari kan harkokin Gabas Ta Tsakiya, na cikin masu ganin cewa Amirka ta gaza a wannan huskar. Kamar yadda ya bayyanar:-

"Amirkawan sun kare kansu ne a wani shaci na birnin Bagadaza. Ba su da wata hulda da al'umman Iraqin, kuma ba su san ko menene ma ke ci wa jama'a tuwo a kwarya ba. A daya bangaren kuma, `yan Iraqin na nuna takaicinsu da bacin ransu ga mamayen da ake yi musu, saboda babu wani mai kulawa da matsalolin da suke huskanta. Ba su kuma san gurin da `yan mmamayen suka sanya a gaba ba. Babu mai tuntubarsu don tattaunawa da su, saboda su Amirkawan, babu abin da suka fi ji da shi sai kare kansu."

Pollock ya kara bbayyana cewa, mafi yawan `yan Iraqin na ganin Amirka za ta janye dakarunta ne, idan matsalolin da suke huskanta suka kara habaka. Yin hakan kuwa na dauke da wata gagarumar kasada, saboda zai kifad da duk yunkurin da shugaban Hukumar da Amirkan ta kafa a Iraqi, Paul Bremer ke yi, wajen mika wa `yan kasar ragamar mulki.

Daya matsalar da Paul Bremern ke ta fama da ita dai, ita ce shawo kan shugabannin darikar shi'iti na kasar da su goyi bayan shirin da ya gabatar. Su dai `yan shhi'itin sun yi watsi ne da shirin da cewar, bai yi la'akari da ka'idojin addinin islama ba. Juan Cole, wani mai nazari kan harkokin da suka shafi addinin islama a jami'ar Michigan, ya bayyana cewa, har abada, `yan shi'itin ba za su taba yarda da wata manufar da Amirka za ta sanya musu a kan dole ba.