Tattaunawa game da hana lulluɓi a Faransa | Zamantakewa | DW | 07.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tattaunawa game da hana lulluɓi a Faransa

Majalisar dokokin ƙasar Faransa ta fara nazarin wani ƙudirin doka da zai hana matan musulmi sanya niƙabi a bainan jama'a.

default

Mata sanye da niƙabi a Faransa

Ƙudirin bai yi amfani da kalaman da ke nunawa a fili cewa Faransa na neman haramta sanya niƙabin a bainan jama'a ba. Maimakon haka jirwaye yayi mai kama da wanka, a inda ya taɓo ƙelle da ke rufe fiska da wasu mata ke amfani da shi a ƙasar. Kana ƙudirin ya kauce ma ambaton musulmi da ma shi kansa addinin musulunci, domin guje ma susa wa mabiya tafarkin addinin rai. Sai dai idan majalisar dokokin ta Faransa da za ta shafe kwanaki biyu tana muhawara ta albarkanci ƙudirin, za a miƙa shi ga majalisar dattijai a watan Satumba mai zuwa domin albarkanta.

A shekara ta 2011 na dokar za ta fara aiki bayan an shafe watanni shida ana naƙaltar da masu sanya niƙabi, hukuncin da ke tattare da haka. Tarar Euro 150 ne, duk matar da za a samu da bijire ma wannan doka za ta biya; yayin da duk na mijin da za a samu da hannu wajen tilasawa mata sanya niƙabi a kan tituna, za a yanke masa hukunci da zai iya kai na ɗaurin watanni 12 a gidan yari, tare da aza masa tarar Euro dubu 30. Ministar shari'a ta Faransa, wato Michele Alliot-Marie, ta ce wannan sabuwar dokar za ta bayar da damar mutunta muradun wannan ƙasa:

Clearstream-Affäre: französische Verteidigungsministerin Michele Alliot-Marie

Ministar Shari'a ta Faransa

"A ƙasar nan, ana rayune fiska a buɗe. Wannan ya na da nasaba ne da muradun ƙasar na mutunci, da yin daidai wa daidai a dukkanin al'amura. Batu ne kuma na gaskiya da riƙon amana."

Ba wata zazzafan mahara da ake fiskanta a zauren majalisar da ke birnin Paris, sakamakon ya da ƙwallo domin rabuwa da ƙuda da wasau jam'iyun adawan ƙasar suka yi. Ko ita ma babbar jam'iyar adawa ta PS ta janye barazanar da ta yi a baya ta haifar da ƙafar ungulu ga yunƙurin na haramta sanya niƙabi. Amma kuma ta ƙaurace ma zaman majalisar kwata-kwata saboda na'am da ƙididdigar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa galibin faransawan na yi da yunƙurin. Ita dai wannan jam'iya ta nunar da cewa, matan da ke amfani da wannan salo na suturta jiki, basu taka kara sun karya.

Kimanin mata 2.000 ne ke sanya niƙami a bainan jama'a, alhali musulmi miliyon biyar zuwa shida ƙasar ta ƙunsa. A hanzari jam'iyar ta gurguzu, kamata yayi gwamanti ta mutunta hukuncin kotun harkokin gwamanti da ya keɓe wuraren da bai kamata a yi amfani da niƙabi ba. Honorable Noel Mamere, ɗan majalisa da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar adawa ta PS yayi tsokiaci da cewa.

Burka tragende Frau in Frankreich

Sauraron bahasin mai sanya niƙabi

" wai shi ya za a aiwatar da dokar? 'yan sanda ne za su shiga cikin ungwani ko ƙaƙa? Shi ya sa mu muka so a taƙaita dokar i zuwa ma'aikatun gwamati kamar su makarantu, da sibitoci da kuma shaguna."

ƙungiyar Amnesty International ta yi kira ga majalisun na Faransa da su yi watsi da ƙudirin, saboda tauye 'yanci mata musamman ma na addini da ya ke yi. Su ma majalisun da ke nazarin mahimman al'amuran ƙasa da kuma ta musulmi sun nuna damuwa game da rikicin da aiwatar da dokar ta haramta sanya niƙabi ka iya haifarwa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu