Tattaunawa da ′yan tawaye a Kwalambiya kan zaman lafiya | Labarai | DW | 19.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa da 'yan tawaye a Kwalambiya kan zaman lafiya

Gwamnati da kungiyar 'yan tawayen ELN za su fara zaman tattaunawar a ranar bakwai ga watan Febrairu mai zuwa a birnin Quito.

Gwamnatin kasar Kwalambiya ta sanar shirin soma tattaunawa da kungiyar tawayen ELN da nufin samar da zaman lafiya a kasar bayan yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar 'yan tawayen Farc, bayan yaki na tsawon shekaru 50. 

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Gwamnatin Kwalambiyar da kungiyar 'yan tawayen ta ELN suka fitar sun ce za su soma zaman tattaunawar a ranar bakwai ga watan Febrarun mai zuwa a birnin Quito. 

Kuma tun a ranar biyu ga watan Febrairu Kungiyar tawayen ta ELN da ke zama kungiyar tawaye ta karshe da ba a kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ita ba a kasar, za ta sako Odin Sanchez Montes de Oca wani tsohon dan majalisar dokoki da ta yi garkuwa da shi a watan Aprilu, a yayin da daga nata bangare gwamnatin Kwalambiyar za ta yi wa wasu daga cikin mambobin kungiyar ta ELN afuwa.