1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa da sojojin RSP masu juyin mulki a Burkina Faso

Salissou BoukariSeptember 22, 2015

Rundunoni daban-daban na sojoji da suka amsa kiran manyan hafsoshin sojan kasar, sun shiga birnin Ouagadougou ba tare da wata matsala ba.

https://p.dw.com/p/1GaC7
Janar Gilbert Diendere
Janar Gilbert DiendereHoto: picture alliance/Photoshot

A halin yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki na RSP kan su ajiye makammansu ba tare da an zubar da jini ba. Rahotanni na cewa, Shugaban kasar na rikon kwarya Michel Kafando ya samu mafaka a ofishin jakadancin kasar Faransa, sannan kuma sojojin sun sallamo Firaminista Laptanan Kanal Isaac Zida da safiyar wannan Talata inda ya koma gidansa na mulki, yayin da a hannu daya kasar Faransa cikin kakkausar murya ta nemi da masu juyin mulkin da su ajiye makammansu.

A wannan Talatar ce dai ake sa ran kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS za ta yi wani zama na musamman a birnin Abuja na Tarayyar Najeriya domin duba wannan lamari duk kuwa da cewa kafin nan ba'a san abun da zai biyo bayan tattaunawar sojojin ba.