1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa a kan shirin nukiliyar Iran

December 11, 2005
https://p.dw.com/p/BvH3

A ranar 21 ga watannan na desamba Tarayyar Turai da kasar Iran zasu tattauna akan shirin nukiliyar Iran, to sai dai fatan da ake da shi kadan ne cewa gwamnatin Teheran zata yi watsi da aikice-aikacenta mai kama da kera makaman nukiliya. Taron wanda zai gudana a birnin Vienna hedkwatar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya zai mayar da hankali ne kan yadda za´a ci-gaba da tattaunawa tsakanin Iran da wakilan tarayyar Turai. A cikin watan agusta aka katse tattaunawar tsakanin kasahen Faransa, Jamus da Birtaniya a madadin kungiyar EU da kuma Iran a daya bangaren. A jiya shugaban hukumar kula da nukiliya a Iran Gholamreza Aghazadeh ya ce kasar sa zata samar da sinadarin uranium da kuma makamashin nukiliya duk da kokarin da kasashen duniya karkashin jagorancin Amirka ke yi na katse mata hanzari.