Tattanawa tsakanin tawagogin Hamas da na Russia | Siyasa | DW | 03.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tattanawa tsakanin tawagogin Hamas da na Russia

An fara zaman taron yini 3 a birnin Mosco tsakanin tawagogin Hamas da na Russia

default

A birnin Moskau na ƙasar Rasha an fara tantanawa tsakanintawagar ƙungiyar Hamas da ta Rasha.

Tawagar Hamas bisa jagorancin shugaban komitin zartsawa na ƙungiyar, Khaled Michael, ta sami gayyata, daga shugaban ƙasar Rasha Vladmir Putin, domin tantanana batutuwa, da su ka jibanci huldodin diplomatia tsakanin Hamas da ƙasashen ƙungiyar Gamayya Turai da kuma Amurika.

Tun bayan zaben 25 ga watan Janairu da a ka gudanar a ƙasar Palestinu, Hamas ta samu gagaramin rinjaye , abinda zai bata damar girka gwamnati, nan da wani lokaci mai zuwa a ƙasar Palestinu.

Jim kadan bayan bayyana wannan sakamako, kasashen turai da Amurika su ka yi ca! ga Hamas, tare da gargadin ta ta yi watsi da matsayin ta na kin amincewa da Israela a matsayin kasa mai cikkakken yanci.Kazalika Hamas, ta kwance damara yaki ta kuma zauna tebrin shawar da hukumomin Israela, domin samar da matakan warware rikicin gabas ta tsakiya cikin ruwan sanhi.

Ba da wata wata ba ,Hamas ta yi watsi da wannan kira.

Sabanin kasashen Amurika, da Gammaya Turai,Rasha ba ta dauki kungiyar Hamas ba, a matsayain yar ta´ada.

Mayar da Hamas saniyar ware, kokuma saka takunkumi ga gwamnatin da zata kafawa ba zai taimaka ba, wajen magance rikicin
 • Kwanan wata 03.03.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1K
 • Kwanan wata 03.03.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1K