1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin Turai na kan turbar cigaba

September 7, 2010

Shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso za baiyana bunkasar tattalin arzikin nahiyar

https://p.dw.com/p/P6Dt
Shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barroso.Hoto: AP

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya shaidawa taron Majalisar Turai cewa ɗaukacin ƙasashe 27 na Ƙungiyar Tarayyar turan sun farfaɗo daga matsalar koma bayan tattalin arziki da duniya ta fuskanta a´yan watannin baya. Barroso wanda ya gabatar da jawabin halin da hukumar ke ciki a zauren Majalisar turan da ke Strasbourg ya ce farfaɗowar tattalin arzikin turan na kan turba ya kuma a sami bunƙasa fiye da yadda aka yi hasashe tun da farko.

A shekarar da ta gabata, matsalar tattalin arziki da ta hada -hadar kuɗaɗe da aka fuskanta ta jefa Ƙungiyarmu cikin gagarumin ƙalubale wanda hakan ya jarraba dogaro na kowace ƙasa daga cikin ƙasashenmu da kuma nuna ƙarfin zumunci da taimakekeniyar da ke tsakanin mu.

Barroso ya ƙara da wajibi ne a ɗauki matakan samar da daidaito a nahiyar mai yawan al´uma fiye da miliyan 500 musamman a tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki a nahiyar kamar Jamus da kuma ƙasashe masu raunin tattalin aziki. Barroso ya kuma gabatar da wasu shawarwari domin kauce wa faɗawa cikin matsalar tattalin arziki a nan gaba.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Yahouza Sadissou Madobi