Tattalin arzikin Najeriya na farfadowa
February 28, 2017Talla
Hukumar kididdigar tattalin arziki ta kasa, ta ce faduwar tattalin arzikin Najeriya na da alaka da faduwar farashin man a kasuwannin duniya da kuma yadda tsageru a kudancin kasar ke fasa bututan mai, da kuma faduwar darajar takardar kudi ta Naira.
Najeriya dai na dogaro ne kacokan a kan arzikin man fetur da Allah ya hore mata, wajen samun kudin shiga. Sai dai kuma gwamnatin Muhammadu Buhari, ta fitar da sabon tsari na fito domin shigar da karin kudi aljuhunta. Wannan ya sa masana ke hasashen komadar tattalin arzikin kasar abana da daidatuwar farashin danyen mai a kasauwannin duniya.