1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tattalin arzikin Jamus a 2006

Jamus zata ci gaba da fama da tafiyar hawainiya ga tattalin arzikinta a 2006

Babu wani canji na a zo a gani da za a samu a shekaru masu zuwa dangane da matsalar nan ta rashin aikin yi da Jamus ke fama da ita. Cibiyar binciken tattalin arzikin Jamus tayi hasashen cewar bana kimanin kashi 9 da rara cikin dari na ma’aikata zasu yi asarar guraben aikinsu a kasar, kazalika a shekara mai zuwa. Dalilin haka kuwa shi ne tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin Jamus ke fama da ita. Domin kuwa ko da yake bana an yi hasashen cewar tattalin arzikin zai samu bunkasar kashi daya da digo bakwai cikin dari, amma wannan ba bunkasa ce da zata dore ba, saboda a shekara mai zuwa bunkasar zata koma kashi daya da digo biyu cikin dari, kamar yadda aka ji daga bakin Klaus Zimmermann, shugaban cibiyar binciken tattalin arzikin Jamus. Dalilin haka kuwa shi ne fafutukar da gwamnati ke yi na cike gibin kasafin kudinta domin cika sharuddan kungiyar tarayyar Turai a cikin gaggawa. Zimmermann ya kara da cewar:

„Gwamnati na bakin kokarinta wajen ta da komadar tattalin arzikin kasa a shekarar nan ta 2006, to amma lamarin da walakin, domin kuwa ta dage akan ci gaba da matakanta na daidaita gibin kasafin kudinta dangane da shekara ta 2007, lamarin da zai yi mummunan tasiri akan al’amuran tattalin arzikin kasa baki daya.

Wani abin da zai dada yin mummunan tasiri akan tattalin arzikin a shekara ta 2007 kuma shi ne shawarar da gwamnati ta tsayar na kara harajin kayan amfanin yau da kullum, wato VAT a turance. Idan wannan manufa ta hadu da tashin farashin makamashi to kuwa ko shakka babu za a samu matsalar hauhawar farashin kaya matuka ainun, kamar yadda aka ji daga Alfred Steinherr daga cibiyar binciken tattalin arzikin ta Jamus, wanda ya ci gaba da bayani yana mai cewar:

Da dai abu mafi alheri ga gwamnati shi ne ta rage yawan harajin dake tattare da albashin ma’aikata, wanda ba shakka zai amfanar da ma’aikata masu karamin albashi. Kuma ko da yake hakan zai yi tasiri akan kasafin kudin kasa, amma a daya bangaren zai kuma taimaka gwamnati ta samu karuwar yawan kudaden haraji a baitul-malinta.

Bana dai gwamnati ta lashi takobin kusantar da gibin kasafin kudinta da sharuddan da KTT ta shimfida, a yayinda a shekara mai zuwa take fatan kayyade gibin zuwa kashi 1 da digo tara cikin dari.