1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin Arzikin Afurka

November 19, 2004

Matsaloli na kyashi da cin hanci da kuma rashin iya gudanarwa suna daga cikin jerin abubuwan dake hana ruwa gudu ga ci gaban tattalin arzikin Afurka

https://p.dw.com/p/BveT

A cikin littafin da ya rubuta karkashin taken: "Shin me ya sanya Afurka ba ta da dogwayen benaye?" David Signer, kwararren masani daga kasar Switzerland ya ba da dalilai da dama, wadanda yake ganin sune ke hana ruwa gudu wajen ci gaban tattalin arzikin kasashen Afurka. Kama dai daga tsafe-tsafe da camfe-camfe da kiyashi da kuma mummunar dabi’ar nan ta maula ko raraka, inda zaka tarar da dimbim mutane sun dogara kacokam akan wani mai wadatar aziki su rika rarakarsa. Duk wani mai arzikin da ba ya sakin hannu zai sha fama da tofin Allah tsine, kuma duk wanda ya yunkura, inda hali za a sake dawo da shi kasa domin yayi daidai da saura. A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa akan haka wani dan kasar Kamaru da ake kira Francis Pagbe dake nazarin kimiyyar tattalin arziki a kasar Moroko cewar:

"Na fito zuwa ketare ne domin neman nagartaccen ilimi ta yadda zan iya kyautata makomar rayuwata a cikin nasara da yalwa, amma fa na yi imanin cewar akwai mutane da dama dake kyashin hakan. Tun da jimawa na dawo daga rakiyar ire-iren mutanen nan dake da akidar cewar duk bakin da Allah Ya tsaga ba zai hana masa abinci ba, a saboda haka suke zama zama su harde kafafuwa don tsammanin warrabbuka. Irin wadannan mutane su ne ainifin masu hasada da kushen duk wani mai kokarin daidaita rayuwarsa. Sune ainifin masu shiga malamai da gidajen boka domin ganin wannan mai kokarin bai cimma nasara ba. Fatansu shi ne duk a hadu a lalace."

Amma fa ba tsafe-tsafe ne ummal’aba’isin koma-bayan tattalin arzikin da Afurka ke fama da shi ba. Misali kasar Kamaru tana daya daga cikin kasashe biyar da suka fi fama da matsalar cin hanci a duniya. Pagbe ya kara da cewar:

"Gwamnati na fama da gibin kasafin kudi. Sanin kowa ne cewar ita gwamnati ta dogara ne kacokam akan kudaden haraji ko kwasta domin samun kudaden shuiga. Amma, misali, idan mutum zai shigo da mota daga wata kasa ta ketare, sai yayi da wajewa tare da jami’an kwasta, inda zai basu toshiyar baka ta CFA miliyan shida, a maimakon kudin kwasta CFA miliyan 200 da zasu kwarara zuwa baitul-malin gwamnati. Shin a haka, ta yaya za a samu ci gaban tattalin arzikin kasa?"

Wani misali a nan dangane son kai na masu fada a ji a nahiyar Afurka shi ne kamfanin sufurin nan na Air Afrique dake karkashin tutar kasashen Afurka da dama, wanda kuma fatara ta rutsa da shi a wasu ‚yan tsirarun shekarun da suka wuce. Daya daga cikin dalilan rushewar kamfanin shi ne kasancewar kowane ma’aikacin jirgin dake da fada a ji kan ba wa ‚yan-uwa da danginsa damar tafiye-tafiye a wannan jirgi ba tare da biyan ko sisin kwabo ba. A wani lokaci zaka tarar da kusan dukkan fasinjojin jirgin dangin wani babban jami’i ne dake da fada a ji, inda za a kai su cefane a Paris ko cinikin wasu hajoji, amma ba tare da sun biya kudin tikiti ba.