1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin Afirka

June 18, 2010

Kayakin da Afirka ke fitarwa zuwa ƙasashe masu samun matsakaicin arzikin masana'antu ya ƙaru

https://p.dw.com/p/Nx7J
Hulɗar ciniki tsakanin Afirka da sauran nahiyoyi musamman Asiya ta bunƙasaHoto: AP

Ana samun ƙaruwar haɗin kan tattalin arziki tsakanin ƙasashen Afirka da sauran ƙasashe masu tasowa da kuma masu samun matsaƙaicin ci-gaban masana'antu na wasu nahiyoyi. Wani rahoton hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya ciniki da ci-gaba wato UNCTAD a taƙaice ya nunar da cewa a shekarar 2008, Afirka ta sayar da kayaki musamman ɗanyun kaya da ma'adanan ƙarƙashin ƙasa da kayan albarkatun noma da kuɗinsu ya kai dala miliyan dubu 283 zuwa ƙetare. A shekarar 1995 a jimilce wannan ciniki bai haura na dala miliyan dubu 34 ba. Abokanen hulɗar cinikin Afirka kamar su China da Brazil suna sayarwa wannan nahiya da kayan da aka sarrafasu. Hukumar ta UNCTAD ta ce ya zama wajibi Afirka ta samar da masana'antun kanta domin 'yantar da kanta daga sayar da ɗanyun kaya zalla zuwa ƙetare.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas