1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon mashaya da masu tabin hankali a Kaduna

Ibrahima Yakubu/LMJMarch 23, 2016

Wani mai maganin gargajiya a Najeriya ya warkar da matasa masu tabun hankali da mashaya miyagun kwayoyi sama da dubu tare da sanyasu rungumar kananan sana'o'in hannu.

https://p.dw.com/p/1IICp
Illar shan miyagun kwayoyi
Illar shan miyagun kwayoyiHoto: picture-alliance/dpa

Mallam Lawal Maduru wanda aka fi sani da suna Mallam Nigga da ke zaman shugaban makarantar gyara tarbiyar matasa mashaya kwayoyi da masu tabin hankali na Aljanu, wato "Nigger Rehabilitation Centre" a Najeriya ya bayyana irin sauyin da ya kawo a cikin kasashen Afirka ga daruruwar matasa da aka kawo su daga kasashen daban-daban domin a warkar da su. Ya ce matasan na fama da nau'in tabin hankali daban-daban, kana bayan sun warke ya na koya masu wasu kananan sana'o'in hannu da zumar magance zaman kashen wando. Malam Lawal Maduru ko kuma Malam Nigga ya ce yana amfani da wasu hanyoyin gargajiya ne wajen bayar da cikakkiyar kulawa ga wadannan marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali, kuma da yawa daga cikin su da ake kawo masa wannan cibiya, matsalar rashin aikin yin ce ta yi musu illar gaske. Tun kafuwar wannan cibiyar kimanin shekaru goma ke nan da suka gabata, matasa da magidanta har ma da tsofaffi maza da mata da kananan yara masu fama da matsalar tabin hankali da iskokai da wadanda shaye-shayen miyagun kwayoyi ta rikirkita musu kwakwalwa masu yawa ne suka sami damar warkewa daga kasashe daban-daban. Kiyasi ya nunar da cewa akalla dalibai sama da 1,600 cibiyar ta sami warkarwa, wadanda kuma ke ci-gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu. Daliban dai sun hadar da mabiya addinan Islama da Kirista. Sana'o'in da cibiyar ke koyar wa sun hadar da kere-keren kofofi da sarrafa na'urar Computer da dinki da saka da yin sabulai, to sai dai babban kalubalen da cibiyar ke fsukanta, shi ne na karancin tallafin daga mahukuntan jihar da ma na kasar baki daya.