1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar yawan jam'iyyun kawance a Nijar

Abdul-raheem Hassan
June 11, 2018

Bangarorin siyasa da na kawancen masu mulki da 'yan adawa na martani kan bullo da sababbin kawancen jam’iyyun siyasa na adawa gabannin babban zaben kasar.

https://p.dw.com/p/2zHxE
Niger Wahlen
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/A. Gillis

Shekaru 27 da suka gabatne Nijar ta samu 'yancin demokradiyya da walwalar kafa kungiyoyi da jam’iyyun siyasa, tun daga lokacin zuwa yanzu daukacin jam’iyyun siyasar da ake kafawa sun dogara ne da gamin gambiza don samun damar madafan iko. Ko da yake lamarin yafi kamari ne bayan samun kawancen jam’iyyu sama da takwas bayan da shugaba Mahammadou Issoufou ya kafa gvwamnati. Dr. Sani Yahaya Janjuna mai sharhi kan al’amurran yau da kullum a Nijar, ya bayyana abin da hakan ke nufi ga makomar siyasa:

Mahamadou Issoufou Premierminister von Niger
Shugaban kasar Nijar, Mahamadou IssoufouHoto: picture alliance/S. Minkoff

"An gano tafiyar jam’iyyar PNDS Tarayya da ke mulki, a yanzu ga tafiyar siyasar jam'iyyar tana so ta goge sauran jam’iyyun siyasa ta yanda a zabukan 2021 masu zuwa, ta kasance ita kadai jam’iyyar ta ishi kanta ba tare da sauran jam’iyyun siyasa sun kama mata ba hakan shi ne ke haddasa yawan kawancen."

Sabon salon tafiyar siyasa ko kuma dabara don tsira da madafun iko ga bangaren jam’iyyun adawa da ake ganin kawancen ya fi yawa a yanzu, na masu kallon batun da cewar kafuwar turbar demokradiyya ce ta tilasta musu yin hakan inji Alh. Doudou Mahamadou kakakin kawancen 'yan adawa a Nijar: "Ko a bangaren masu mulki akwai kawance, idan har ba demokradiyya me ya kai ga kafa kawancen jam'iyyu.? Ai ba a biyan mu kudi, amma ana yi ne saboda akida da kare mutunci shi ne ya kai mu ga shiga irin wannan tsarin."

Ibrahim Yacouba Außenminister Niger
Tsohon ministan harkokin wajen Nijar, Ibrahim YacoubaHoto: DW/A. M. Amadou

Sai dai kakakin kawancen jam’iyyun da ke Mulki MRN Assoumana Mahamadou na ganin duk da matsalar yawan kawance irin na 'yan adawa, na faruwa ne sakamakon rashin iya tafiyar da tsari a cikin tafarki na adawa: "Ai mu muka yi adawa ta gaskiya muka bai wa tsohon shugaban kasa Tandja dama ta yin mulki a cikin kwanciyar hankali, kuma inda bai yi ba mu bayyana cewar bai yi ba inda kuma yayi mai kyau mu yaba. To amma su sun haukace ne saboda kwadayin mulki duk abin da aka yi sai su ce bai yi ba." 

Masu nazarin siyasa na nuna shakku kan makomar dimokradiyyar Nijar, ganin yadda ake ci gaba da bullo da sababbin kawancen jam'iyyun siyasa gabanin babbar zabe. Yanzu haka dai Nijar na da kawancen jam’iyyun siyasa da na 'yan farar hula barkatai daga cikin wasu tarin jam’iyyu 107 din da ke kasar, duk da yake jam'iyyun da ke da wakilci a cikin majalisar dokoki ba su wuce takwas ba.