Tasirin Brexit a kasar Birtaniya da Afirka | Zamantakewa | DW | 23.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tasirin Brexit a kasar Birtaniya da Afirka

Wasu kasashen Afirka rainon Ingila ciki har da Najeriya sun fara nazarin illa ko ci gaban da ke tattare da matakin da Birtaniya ta dauka na mika takardar shirin ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Kasar Birtaniyar ta mika takardar shirin barin Kungiyar Tarayyar Turai watanni tara bayan da al'ummarta suka kada kuri'ar raba gari da EU. Bangarorin biyu za su shafe shekaru biyu suna tattaunawa tsakaninsu don cimma matsaya kan yadda dangantakarsu zata kasance a fannin tattalin arziki da shige da fice.

A kasar Ghana da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka, jama'a na tofa albarkacin bakinsu kan ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai. Yayin da a Najeriya kuwa, aka fara duba tasirin da wannan mataki na Birtaniya zai haifar wa kasashen Afirka

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin