1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin zaune tsaye a Iraqi

February 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7F

Dubbannin mabiya darikar shi´a a iraqi sun hau kann titunan garin Samarra suna gudanar da zanga zangar nuna fushin su ga wani hari da aka kai kann kaburburan jikokin manzon Allah SAW, wato Imam Hassan da Hussain.

Rahotanni dai sun nunar da cewa harin na bom ya haifar da lalata wani bangare na cikin wadannan kaburbura guda biyu.

Jami´an yan sanda dai sun zargi mabiya darikar Sunni ne da dasa bom din daya tashi a wannan guri dake a zaman gurin Ibada mafi girma ga mabiya darikar shi´a.

Tuni dai Faraministan kasar Ibrahim Al Jafari ya bayar da hutun kwanaki uku na zaman makoki, a sakamakon faruwar wannan abu.

Bugu da kari Faraminista Ibrahim Al Jafari da kuma Jack Straw, ministan harkokin wajen Biritaniya wanda ke ziyara a kasar a yanzu, dukkannin su sun yi Allah wadai da wadanda suka kai wannan hari.