1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin wani bam a birnin Bagadaza yau da safen nan ya janyo asarar rayukan mutane biyu.

Rahotannin da ke iso mana daga birnin Bagadaza sun ce mutane biyu ne suka rasa rayukansu nan take, sa’annan wasu 9 kuma suka ji rauni, yayin da bam ya tashi cikin wata mota kusa da ofishin kamfanin wutar lantarki na birnin. Wata sanarwar da ’yan sandan birnin suka bayar kuma ta tabbatar da rahotannin. Wani jami’in ’yan sandan, 1st Laftanan Thaer Mahmoud ya ce bam ɗin ya tahsi ne a unguwar Hurriya a birin na Bagadaza. Sai dai bai ba da wani ƙarin bayani kuma.