1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin tagwayen boma bomai a Iraki

Zainab A MohammadMay 30, 2005

Iraki na cigaba da fuskantar rikice rikice.......

https://p.dw.com/p/Bvbc
Hoto: AP

A yau ma dai kamar yadda ya zamo alada a Iraki,wasu yan kunar bakin wake biyu sun tayar da jigidan boma bomai da suka daura tsakiyar tsofin jamian yansanda dake wata zanga zanga a garin hilla dake kudancin birnin bagadaza,harin daya ritsa da rayukan mutane 27,banda fiye da dari da suka jikkata.

Wannan harin na yau daya wakana a wannan gari dake dauke da mafi yawan yan darikar shia ,da kuma rahotan cafke shugaban jammiyar yan darikar sunni da yayansa uku da sojin Amurka sukayi da asubahin yau a wani mamaye da suka afkawa gidansa da ita,ya tayar da wani sabon rikici da sabani tsakanin yan kasar ta iraki.

A hannu guda kuma kungiyar Alqaeda dake Irakin ta dauki alhakin kai wadannan tagwayen hare hare,a wani sako data aike ta yanar gizo gizo watau Internet.

Rahotan jamian tsaro dai na nuni dacewa wadannan yan kunar bakin wake sun hade ne cikin yamutsin tsoffin yansanda dake zanga zanga a kofar maaikatar gwamnati dangane da watsar da shiyyansu da akayi.

Na farkon dai yatayar da jigidan boma bomai a tsakiyar mutane,ayayinda na biyun ya hade da wadanda ke gudu kafin shima ya tayar da nasa.

Yan sanda sun sanar dacewa saida aka rika tsintan bangarorin mutane da suka tarwatse sakamakon tashin wadannan boma boman.

Tun da aka sanar da sabuwar majalisar gudanarwa a karkashin jagorancin yan darikar Shia a ranar 28 ga watan daya gabata a Iraki,aka cigaba da fuskantar hare haren boma bomaui zuwa harin kwanton bauna,wanda ya zuwa yanzu gididdiga na nuni dacewa sama da mutane 700 suka rigamu gidan gaskiya.

A bangaren dakarun Amurka kuwa,wannan wata da muke ciki na mai kasancewa mafi muni a garesu domin jamiansu 70 ne suka bakunci lahira a Irakin.

A kokarinta na ganin cewa ta samu goyon bayan alummar kasar tun bayan kifar da gwamnatin sadam Hussein,Gwamnatin Irakin ta kaddamar da wani shiri na farautar yan yakin sari ka noke a wannan kasa musamman a birnin Bagadaza da kewaye.

Jamian Irakin sunyi nuni dacewa kimanin dakarun kasar dubu 40 zasu like dukkannnin hanyoyin shiga birnin Bagadaza ayayinda wasu zasu shiga sako sako a gunduwowi domin kamun yan yakin sari ka noken,wanda aka fara gudanarwa jiya lahadi.

Kungiyar Alqaeda a karkashin jagorancin Abu Musab al-Zarqawi tace ta mayar da martani dangane da wannan shirin mamaye da aka kaddamar a jiyan.A jiyan dai yan yakin sunkuru sunyi arangama da jamian yansandan Iraki a yammacin bagadaza,ayayinda a hannu guda kuma suka tayar da boma bomai daban daban har uku a motoci.A sauran sassam kasar kuwa yan yakin sari ka noken sun kai hare hare a jiya lahadi inda suka kashe yan irakin 25 da sojin Britania guda,inji majiyar jamian tsaron kasar.