1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin nakiya ta yi sanadiyyar rasa rayuka a Rivers da ke Najeriya

May 17, 2012

Wata nakiya da aka ɗauko cikin wata mota ƙirar safa ta tarwatse a garin Fatakwal, fadar gwamnatin jihar Rivers da ke kudu maso kudancin tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/14x5C
Hoto: picture-alliance / dpa

Nakiyar dai ta fashe ne a unguwar Rumuokoro da ke tsakiyar garin na Fatakwal kuma ta yi sanadiyyar rasuwar mutane kimanin uku tare da jikkata wasu.

A zantawarsa da kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP ta wayar tarho, gwamnan jihar ta Rivers Rotimi Ameachi ya tabbatar da aukuwar tashin nakiyar.

Tuni dai aka aike da da jami'an tsaro yankin da abin ya faru domin kilkace wajen kamar yadda Lutanan Kanar Onyema Nwachukwu na rundunar sojojin Najeriya a Fatakwal ɗin ya shaidawa manema labarai sai dai bai yi karin haske gama da lamarin ba.

Yankin kudu maso kudancin na Najeriya, inda garin na Fatakwal ya ke, ya sha fama tada ƙayar baya irin ta tsagerun Nija-Delta game da batun samun kaso masfi tsoka na arziƙin man fetur ɗin da ke yanki ke da shi, kafin daga bisani gwamnatin ƙasar ta daidaita da su a shekara ta 2009 a wani shiri da aka yi na yi mu su afuwa, sai dai wannan shi ne karo na farko da aka samu wannan tashin nakiyar a yankin.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman