Tashin hankula a Birtaniya | Siyasa | DW | 24.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tashin hankula a Birtaniya

Mutun daya yayi asarar ransa sannan wasu 35 suka ji rauni sakamakon tashin hankula na kabilanci a Birtaniya

Tashintashina a Birmingham

Tashintashina a Birmingham

An yi kwanaki da dama ana fama da zaman dardar tsakanin matasa bakar fata da takwarorinsu ‚yan usulin Asiya kafin tashintashinar ta barke a wata unguwa ta ‚yan rabbana ka wadata mu dake garin Birmingham, wanda shi ne na biyu wajen girma a kasar Birtaniya. Amma duk da haka jami’an tsaro na ikirarin cewar wai babu wata alamar da ta nuna yiwuwar barkewar tashe-tashen hankula ballantana a dauki wani matakin dakatar da shi. A lokacin da yake bayani wani kakakin ‚yan sandan cewa yayi:

Jami’an tsaro na matukar bakin ciki a game da cewar daya daga cikin mazauna yankin yayi asarar ransa da kuma kasancewar an kai farmaki kann wadanda ba su san hawa ba ba su san sauka ba abin da ya hada har da jami’an tsaro.

Amma fa shi kansa kakakin ‚yan sandan sai da yayi nuni da cewar ba wanda yayi zaton cewar rikicin zai tsamari ya dauki irin wannan salo na kisan kai, inda ya kai ga halaka wani dan shekaru 23 da haifuwa da kuma ji wa wasu mutane 35 rauni. An dai tsare wasu mutane biyu sakamakon wata musayar wutar da aka fuskanta a jiya lahadi ko da yake jami’an tsaron ba su tabbatar da ko shin lamarin na da alaka da tashintashinar ba, wadda kafofin yada labaran Birtaniya suka ce ta faru ne sakamakon dalilai na banbancin launin fata. Wasu da suka gane wa idanuwansu abin dake faruwa sun dora laifin akan wani gungu ne na matasa ‚yan usulin Asiya su kimanin 100, wadanda suka fara ta da zaune tsaye. Da farko dai sai da jami’an tsaro da ‚yan siyasa suka hallara domin tattaunawa da bangarori dabam-dabam na ‚yan kaka-gida domin neman haske a game da zargin da ake wa wasu ‚yan usulin Asiyan na yi wa wata ‚yar usulin Jamaika dake da shekara 14 da haifuwa fyade. Wannan zargin ya haddasa zanga-zanga mai tsanani tare da arangama tsakanin bakar fata da ‚yan usulin Asiya a makon da ya wuce. To sai dai kuma ita kanta yarinyar da ake ikirarin yi mata fyaden har yau ba a gano ta ba duk kuwa da shela da jami’an tsaro suka rika yi. Akwai rade-radin cewar yarinyar tana zaune ne ba a bisa ka’ida ba a kasar Birtaniya kuma tana tsoron ka da a cafke ta a nemi komawa da ita gida. An dai taba fuskantar irin wannan tashintashina a Birgmingham misalin shekaru 20 da suka wuce. A wancan lokaci sai da aka yi tsawon mako guda kafin jami’an tsaro su samu kafar lafar da kurar rikicin.