1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankalin a Somaliya

September 23, 2010

Ana ci gaba da rasa rayuka a ƙasar Somaliya, inda wani sabon tashin hankalin ya hallaka matune da yawa a yau.

https://p.dw.com/p/PLKV
Ma'aikatan lafiya a Somaliya ke jan gawaHoto: AP

A ƙasar Somaliya wani sabon tashin hankali ya barke, inda ƙungiyar Alshabab ta ƙaddamar da hari a birnin Mogadishu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 22. Jami'an kiwon lafiya da shaidu sun bayyana cewa wannan sabon tashin hankalin ya raunata mutane da dama. Masu tada ƙayar bayan sun kai hari a wuraren da dakarun gwamnati da kuma waɗanda ke hannun dakarun kiyaye zaman lafiya hari. Shugaban Ayyukan gaggawa na birnin Mogadishu Ali Musa yace "Mun samu gawakin mutane 22, kana a ƙalla wasu 80 sun samu raunuka". Ali Musa yace aksarin waɗanda suka mutu fararen hula ne da suka samu rauni, bayan da dakarun gwamnati da na ƙasashen Afirka masu kiyaye zaman lafiya suka maida martani, inda yace sunyi ta cilla rokoki a wurin da ke cike da jama'a, inda ya kwatanta harin da ayyukan dabbanci. Yanzu dai angyasta cewa kimanin mutane dubu 21 suka mutu tun shekaru uku bayan da Amirka ta hamɓare gwamantin masu biyayya ga kotunan shari'a suka kafa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal