Tashin hankali a Thailand
May 19, 2010Tankokin sojin gwamnatin Thailand sun fara ragargaza shingayen da masu adawa da gwamnati da ke bore suka kafa a cibiyar kasuwancin ƙasar dake Bangkock. Gwamnatin ƙasar ta ƙira masu zanga zangar da su yi sorenda nan take. Dubban masu boren waɗanda aka sani da masu jajayen riguna, har yanzu ke fake a sansanonin da suka kame a cikin babban birnin ƙasar. Kakakin gwamnatin ƙasar ya bayana cewa, " Domin mu samu kawo ƙarshen tashin hanklin da ya ɓarke a 'yan kwanakinnan mun keɓe wassu wurare, waɗande dole a samar da tsaro, kuma za mu samar da tsaro ga al'umma." Wannan matakin basani ba sabo da soji suka fara ya zo ne bayan da tattaunawa tsakanin gwamnati da masu boren ta bi ruwa, yanzu dai kwana biyar kenan ana arangama tsakanin sojoji da masu neman a sauke gwamnati, abinda ya hallaka mutane kimanin 40.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasiru Awal