Tashin farashin mai na baranaza ga tattalin arzikin duniya | Labarai | DW | 22.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin farashin mai na baranaza ga tattalin arzikin duniya

A dangane da tashin farashin mai da ba´a taba ganin irinsa ba a duniya, kasashen kungiyar G7 masu arzikin masana´antu sun yi kira da a kara zuba jari wajen samar da danyen mai tare da yin tsumulmular makamashi. Bayan wani taro da suka gudanar a birnin Washington ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashen kungiyar ta G7 sun yi gargadin cewa duk da kyawawan alamun farfadowar tattalin arzikin duniya, har yanzu farashin man na zama babbar barazana ga tattalin arzikin duniya baki daya.jim kadan gabanin taron farashin mai ya haura dala 75 a kowace ganga. Ministan kudin tarayyar Jamus Peer Steinbruck ya janyo hankali game da takadamar nukiliyar Iran da cewa rikicin yankin GTT ka iya yin mummunan tasiri ga farashin mai.