1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TASHIN BOMA BOMAI A YAYIN ZIYARAR COLIN POWELL A IRAQI.

Maryam L.Dalhatu.July 30, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhf

Sakataren harkokin wajen kasar amurka,Colin Powell,a yanzu haka yana birnin bagadaza a kasar iraqi,wadda wannan ziyara itace ta uku da ya kai kasar tun bayan da amurka ta mamaye kasar ta iraqi a shekarar data gabata.

Mr Colin Powell,ya kai wannan ziyara ne don tattaunawa akan harkokin tsaro a kasar ta iraqi,musamman ma don ganin yadda tashe tashen hankula ke dada rincabewa a koina cikin kasar.

A jawabin da yayi a yayin ganawarsa da shugaban kasar iraqin,Ghazi Al-Yawar,Mr Powell,ya jaddada niyyar amurka na cigaba ta aiki hannu da hannu da gwamnatin rikon kwarya a iraqin wajen yakar yan taadda,tare kuma da tabbatuwar zaman lafiya a kasar baki daya.

Wannan ziyara ta Mr Powell ta kasance ta farko da wani babban jamiin amurka ya kai kasar iraqin tun bayan da aka mikawa yan kasar mulkinsu a hannu.

A nasa jawabin shugaban kasar iraqi,Ghazi Al-Yawar,ya bayyana karfin dangantakar dake akwai tsakanin kasashen biyu wato amurka da iraqin,inda yake cewa,babu shakka amurka masoyiyar iraqi ce musamman ganin yadda amurkan ta tashi haikan don ganin an samu zaman lafiya a iraqi.

A hannu guda kuma shugaban kasar ya mika jinjina ga jakadan amurka dake kasar iraqin Mr Negrapote,kamar yadda ya musanta zargin da akewa jakadan da cewa yana neman ya dinga jan akalar gwamnatin iraqin don yin abinda yake so,inda yake cewa Mr Negroponte na aiki tukuru a wannan kasa,kamar dai yadda kowane jakada ke aiki a koina a duniya.

A karshe ne kuma shugaban kasar ke bayyanawa Mr Powell,matakan da gwamnatin kasar iraqi ke shirin dauka don tabbatar da cewa an gudanar da zaben dake karatowa cikin kwanciyar hankali a kasar a watan janairu na shekara mai zuwa.

Kwanaki biyu kenan da wannan tashin bomb din na garin baquba,wanda rahotanni a yanzu ke bayyana cewa yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dari da ashirin,a yau kuwa a yayin da sakatare Colin Powell ke ganawa da shugaban kasar iraqin,boma bomai hudu ne suka tashi a wurare daban daban a wannan birni da yake wato bagadaza.

Har yanzu dai dakarun sojin amurkan dake bagadaza,basu gano musabbabin tashi wadannan boma bomai ba,sai dai kuma rahotanni sun bayyana cewa babu wani daya rasa ransa ko kuma ya jikkata.

A wata sabuwa kuma a daren jiya mutane goma sha uku ne suka rasa rayukan su wasu goma sha hudu kuma suka raunana,sakamakon wani dauki ba dadi daya gudana a tsakanin sojin amurka da kuma yan tawaye.a garin falluja,dake yammacin birnin bagadaza.

Har ila yau wannan dauki ba dadi yayi sanadiyyar kona shagunan makanikai guda goma sha biyu,da kuma gidaje guda biyu.

A wata tattaunawa data gudana ranar alhamis a kasar saudi arabiya tsakanin mahukuntan kasar da prime ministan iraqi Iyad Allawi,da kuma sakataren amurak Colin Powell,sun yi kira ga kasashen larabawa dasu tura dakarun su izuwa kasar iraqi,don bada nasu tallafin wajen samar da zaman lafiya a kasar.

A yau ne kuma wata sanarwa daga yan kungiyar al qaeda ta biyo bayan wannan mataki da kasashen larabawan ke shirin dauka,inda suka yi gargadi ga kasashen larabawan da kada su kuskura su tura sojin su iraqin,tare da barazanar daukar kwakkwaran mataki kann duk kasar data tura dakarun nata.