1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TASHIN BOMA BOMAI A KASAR IRAQI.

Maryam L.Dalhatu.July 28, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhi

A kasar iraqi,kamar yadda rahotanni daga kamfanin dillancin labaru na AFP suka bayyana,kawo yanzu da gwamnatin rikon kwarya a kasar iraqin ke cika wata guda da karbar mulki,hankali bai kwanta ba a kasar,domin kuwa ana nan ana ta fuskantar tashe tashen hankula a koina cikin wannan kasar.

A yau dai rahotanni da suka iso mana sun tabbatar da cewa,sama da mutane hamsin ne suka rasa rayukan su a kofar wani ofishin yan sanda,a birnin bagadaza,sakamakon tada bomb da wani dan kunar bakin wake yayi a wannan wuri.

Wannan bomb dai ya tashi ne a lokacin da wata mota cike da mutane tazo wucewa ta gaban ofishin yan sanadan,bisa hakan ne kuma ake zargin cewa akwai dan kunar bakin wake a cikin wannan mota.

A garin kirkuk dake kasar kuwa a yammacin jiya talata,mutane goma sha daya ne suka rasa rayukan su sakamakon wani dauki ba dadi daya gudana a tsakanin dakarun sojin kasar da kuma yan tawaye.

A cewar wani jamiin kamfanin dillancin labaru na AFP,wanda ya ganewa idansa,yace yaga gawawwaki akalla goma sha biyu a kofar wani asibiti dake garin baquba,bayan da wani bomb ya tashi a wannan gari.

Kakakin ministan harkokin cikin gidan kasar iraqi,mai suna Sabah Kahdim,ya bayyanawa manema labaru cewa wannan tashin bomb na garin baquba,ya raunata mutane kusan arbain,tare kuma da halaka mutane sittin da takwas a yanzu,sai dai kuma babu tabbacin cewa wadannan da suka raunana zasu rayu.

A tun lokacin da amurka ta tura sojin ta kasar iraqi a watan maris na shekara ta dubu biyu da uku,kawo yanzu,kimanin sojin nata dari shida da sabain ne suka rasa rayukan su.

Bayan da kasar phillipines ta janye dakarun ta daga kasar don ceto dan kasar tata daya da yan tawayen sukai garkuwa dashi,a yanzu kuma kasar jordan ta bayyanawa kasar amurka tata niyyar ta janye nata dakarun daga iraqin don ceto yan kasar ta biyu da yan tawayen sukai garkuwa dasu.

Wannan rana dai a kasar iraqi,ta kasance ranar bakin ciki,bisa wannan mummunan hadari daya afku a garin baquba,domin kuwa tun ranar ashirin da hudu ga watan daya gabata da tashin wani bomb yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dari,sai yanzu aka sake samun wani hadarin da aka rasa rayuka da yawan haka.

Rahotanni daga kasar amurka,na bayyana dalilin zaman ta a kasar iraqi har yanzu,wanda baya ga samar da zaman lafiya,suna nan ne don gyara kasar ta iraqi.a cewar Admiral David Nash,wani babban jamiin amurka dake kula da bada kwangiloli a kasar iraqi,kasar amurka ta fidda kudi har dalar amurka,billion goma sha takwas da digo hudu,don tada komadar kasar.

A cikin wannan kudi kuwa a yanzu an kashe kimanin kashi biyu a cikin dari na kudin don fara gudanar da wannan aiki.

Duk kuwa da wannan tashe tashen hankula dake faruwa a kasar ta iraqi,ministan tsare tsaren kasar,Mehdi Al-Hafez,yana can kasar saudi arabiya,inda ya kai ziyara don ganawa da takwaransa na wannan kasa,kann batun dawo da huldar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

A tun shekaru goma sha uku da suka wuce ne,shugaban kasar iraqin na wannan lokaci,saddam husseini,ya yanke wannan hulda ta cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

Maryam L.Dalhatu.