1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin bom a Punjab yayi ajalin mutane 6

October 15, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8U

Mutane 6 sun rasa rayukan su, wasu kuma da dama sun jikkata a India, bayan tashin wani bom.Rahotanni sun ce bom din ya tashi ne a cikin wani dakin wasan kwaikwayo dake yankin Punjab.Wannan dai shine karo na biyu a cikin mako daya da yankin ya fuskanci irin wannan hari.Jami´an yan sanda na yankin sun tabbatar da cewa hari ne na yan ta´adda , to amma basu fadi sunan wani ko kungiyya dake da hannu a ciki ba.