Tashin bom a kasar Afghanistan | Labarai | DW | 05.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bom a kasar Afghanistan

Wani dan kunar bakin wake dauke da bom a cikin motar sa ya fada a cikin cinci rindon jami´an yan sanda a kasar Afghanistan, inda nan take yan sanda 10 suka ce ga garin ku nan.

Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa wasu yan sandan goma sun samu raunuka iri daban daban a sakamakon afkuwar wannan abu.

Wannan dai al´amari a cewar kamfanin dillancin labaru na Reuters ya faru ne a garin Tirin Kot dake yankin Uruzgan.

A waje daya kuma, mbayanai daga Turkiyya sun nunar da cewa Shugaba Hamid Kharzai na Afghanistan ya isa kasar don fara ziyarar aiki.

Wannan dai ziyara na a matsayin irin ta farko daga wajen wani shugaba a Afghanistan a matsayin shekaru 48 da suka gabata