Tashin bom a Iraq | Labarai | DW | 10.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bom a Iraq

Mutane a kalla 30 ne suka rasa rayukan su a can kasar Iraqi sakamakon tashin wani bom a cikin wani gidan cin abinci a birnin Bagadaza. Ba a da bayan haka wasu mutanen da yawa ma sun samu raunuka iri daban daban.

A cewar wasu jami´i na kasar, dan kunar bakin waken ya tashin bom din ne jim kadan da shir sa a cikin otal din cin abincin dake tsakiyar birnin na Bagadaza.

Ya zuwa yanzu dai tuni kungiyyar Alqeeda dake da reshen ta a Iraqi tayi ikirarin cewa itace ta kai wannan hari na kunar bakin waken.

A waje daya kuma wasu bayanai da suka iso mana daga kasar ta iraqi na nuni da cewa wasu mutanen a kalla shida suma sun rasa rayukan nasu sakamakon tashin wani bom a kofar daukar ma´aikatar daukar sabbin soji dake yankin Tikirit