1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bom a birnin Tel Aviv na Israela

Wani dan kunar bakin wake ya tashi bom din dake jikin sa, a cikin cin ci rindon mutane kusa da wata tashar Bus dake birnin Tel Aviv na kasar Israela.

Hakan dai a cewar bayanai yayi sanadiyyar jikkata mutane nan take kusan 30. To sai dai ya zuwa yanzu babu bayanin asarar rai koda guda daya.

Wannan dai hari ya kasance irin sa na shida da aka kawo a kasar ta Israela a tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaitawa da bude wuta a watan fabarairun shekarar data gabata.

Ya zuwa yanzu dai kungiyyar masu tsattsauran ra´ayi ta Islamic Jihad ce tayi ikirarin kai wannan hari na yau.

A daya barin kuwa, shugaban yankin Palasdinawa, Mahmud Abbas cewa yayi wannan hari ba wani abu zai haifar ba illa zagon kasa ga zaben yan majalisun dokoki da yankin ka shirin aiwatarwa a ranar 25 ga watan nan da muke ciki.