1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bama bamai guda uku a Bagadaza

Mutane a kalla goma ne suka rasa rayukan su wasu kuma sama da dozin daya suka jikkata a can kasar iraqi.

Hakan kuwa ya biyo bayan wani harin bama bamai ne da yan fadan sari ka noke suka kai hotal din Palastine dake birnin Bagadaza.

Rahotanni dai sun nunar da cewa an jiyo karar fashewar wasu abubuwa a kalla guda uku,wanda nan take hayaki ya turnuke sararin samaniya.

Ya zuwa yanzu dai ba a gano wadanda suka aikata wannan danyan aikin ba ballantana dalilin aikata hakan.