1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashen tashen hankulan kabilanci a Kenya

Gwamnatin shugaba Mwai Kibaki ta ɗorawa abokin adawa Raila Odinga laifin haddasa rikicin kabilancin da ya addabi ƙasar, wanda yayi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 250. Kakakin gwamnati Alfred Matua ya ce kawo yanzu magoya bayan Odinga ne kaɗai ke ta da ƙayar baya inda ya zarge su da aikata kisan ƙare dangi akan kabilar Kikuyu.

Matua:

Ya ce “Muna jin wata dubara ce ta ƙoƙarin rarraba kawunna ´yan ƙasa ta hanyar ingiza mutane su ta da tarzoma domin ɗora wasu kan iko ta ɓarauniyar hanya. Bisa wannan dalili aka tsaurara matakan tsaro a birnin Nairobi. Za a yi maganin ƙungiyoyin nan na ´yan banga.”

A jiya akalla mutane 30 suka ƙone har lahira lokacin da wasu ´yan banga suka cunnawa wani coci wuta a yammacin Kenya.