Tashe-tashen hankulla na ta ƙara haɓaka da janyo asarar rayukan mutane a Iraqi. | Labarai | DW | 23.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe-tashen hankulla na ta ƙara haɓaka da janyo asarar rayukan mutane a Iraqi.

Wani jerin tashin bamabamai cikin motoci da farmakin rokoki a wata unguwar mayaƙan ’yan dariƙar shi’iti a birnin Bagadaza, sun janyo asarar rayukan a ƙalla mutane 75. ’Yan sandan birnin sun ce, wasu mutane kimanin 80 ne kuma suka ji rauni a hare-haren da aka kai yau ɗin a unguwar Sadr City da ke birnin Bagadazan. Amma wata sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gidan Iraqin ta bayar, ta ƙiyasci cewa yawan rayukan da suka salwanta a birnin yau kawai, ya kai a ƙalla ɗari da 15, sa’annan yawan waɗanda suka ji rauni kuma ya kai ɗari da 25. Har ila yau dai, rahotanni sun ce, wasu ’yan bindiga kimanin su 30, sun kai wani harin kuma a kan wani gini da jami’an ma’aikatar kiwon lafiyar ƙasar ke aiki a cikinsa. Wani kakakin ma’aikatar ya ce masu kai harin sun ci ɗamara ne da mashingan da kuma rokoki. Babu dai ƙarin haske game da asarar rayuka ko na kadarori da wannan harin ya janyo.