Tashe-tashen hankulla na ta ƙara haɓaka a ƙasar Sri Lanka. | Labarai | DW | 18.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe-tashen hankulla na ta ƙara haɓaka a ƙasar Sri Lanka.

A ƙasar Sri Lanka, ana ta ƙara samun haɓakar tashe-tashen hankulla, sakamakon ɓarkewar wata sabuwar fatfatawa tsakanin dakarun gwamnati da ’yan tawayen ƙungiyar na ta Tamil Tigers. Wani kakakin ’yan sandan ƙasar ya ce ’yan tawayen sun bindige jami’an tsaro 3 har lahira, a wani kwanton ɓaunar da suka yi musu a arewacin tsibirin. A nasu ɓangaren, ’yan tawayen sun ce dakarun gwamnatin ne suka kai musu hare-hare a wasu yankunan. Wannan sabon rikicin kuwa, ya biyo wata mummunar fafatawa ne da ɓangarorin biyu suka yi da juna a teku da kuma ƙasa jiya, inda kusan mutane 50 suka rasa rayukansu. Tun ran alhamis da ta wuce dai, an ƙiyasci cewa fiye da mutane ɗari ne suka rasa rayukansu, a wani mummunan tashin hankalin da ba taɓa gani a ƙasar ba kuma, tun lokacin da aka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a shekara ta 2002, don kawo ƙarshen yaƙin basasan da aka shafe fiye da shekaru 20 ana yi.

Su dai ’yan ƙungiyaer ta Tamil Tigers, suna fafutukar samun ’yancin yankunan arewacin kasar ne daga sauran tsibirin na Sri Lanka.