1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankulla a yankin Kivu

May 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuKK

Tawagar Majalisar Dinkin Dunia a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ta bayyana taɓarɓarewar zaman lahia, a yankunan kudu da arewancin Kivu.

A tsukin kwanaki 2 da su ka gabata, yan tawaye sun hallaka kimanin mutane 20 a wannan yanki.

Wanda su ka ganewa idon su al´amarin, sun ɗora alhakin wanan hari ga ƙungiyar tawayen FDLR.

Wannan ƙungiya mai sansani a gabacin Jamhirya Demokradiya Kongo, ta ƙunshi a ƙalla mayaƙa dubu 10, da su ka kutso, daga Rwanda, tun shekaru 13 a baya.

A dangane da hauhawar tashe-tashen hankulla a yankin, yan majalisar dokokin Kivu, ta bakin kakakin su Bahati Bichengira,sun yanke shawara ƙauracewa majalisar, domin nuna fushin, a kann abun da su ka kira, ɗaukar sakainar kashi, da gwamnati kewa batun tsaro a yankin Kivu.