Tashe-tashen hankulla a Najeriya | Zamantakewa | DW | 22.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tashe-tashen hankulla a Najeriya

Tashe-tashen hankullan baya-bayan nan da aka yi a Najeriya, wanda aka fara a biranen arewa guda biyu, sun yadu zuwa har kudancin kasar, inda aka yi asarar rayukan jama'a da dama, a galibi, wadanda ba su san hawa ko sauka ba. hauhawar tsamarin da ake samu dai, wani abin damuwa ne ga jama'ar kasar da ma ga sauran duniya baki daya, saboda muhimmancin da Najeriya ke da shi a halin yanzu, a harkokin siyasa da na tattalin arzikin kasa da kasa.

Shugaba Olusegun Obasanjo na tarayyar Najeriya.

Shugaba Olusegun Obasanjo na tarayyar Najeriya.

Tabbas ne dai cewa, zanga-zangar da aka yi ta yi, wato na nuna ɓacin ran musulmi ga zanen ɓatancin da aka yi wa addininsu, ba su ne dalilan rikicin da ya janyo ƙone-ƙone da asarar rayukan jama’a a birane da dama na Najeriya ba. Akwai dai masu sha’awar ta da zaune tsaye da yawa, waɗanda suka shiga cikin irin wannan zanga-zangar don yin amfani da addini ko kuma ƙabilanci wajen cim ma burinsu. An fi samun irin waɗannan mutanen ne kuwa a wuraren da aka fi fama da matsalolin tattalin arziki da matsin halin rayuwa na yau da kullum. A arewacin ƙasar dai, inda musulmi suka fi rinjayi, jama’a da dama na ganin cewa tun da shugaba Obasanjo ya hau karagar mulki ne, a hankali aka yi ta mai maslaharsu a baya, ban da fa’idar da yankunan kudancin ƙasar ke da ita a huskar tattalin arziki. Kazalika kuma, a yankin Niger-Delta mai arzikin man fetur, mazauna na bayyana ra’ayin cewa, bayan shekaru 7 na mulkin dimukraɗiyya, babu wani ci gaban da suka samu.

Rikice-rikicen da suka ɓarke da farko a arewacin ƙasar inda aka kai wa kiristoci hari, sa’annan a wani matakin mai da martani kuma, kiristoci a kudu suka afka wa muslmi; da kuma gwabzawar da `yan tawaye ke yi da jami’an tsaro a yankin Niger-Delta, na nuna cewa kawo yanzu, mahukuntan siyasa na Najeriyan ba su da wata dabara ta samo bakin zaren warware matsalar da ke barazana ga makomar ƙasar gaba ɗaya. A fagen siyasa da kuma fannin tallin arziki dai, kowa na ƙoƙarin samar wa kansa da iyalansa fa’ida ne kafin a ji da abin da ƙasa gaba ɗaya ke ciki. Masu gwagwarmayar azurta kansu a wannan fafutukar kuwa, ba su damu ba da abin da zai auku, ko da ma yaƙin basasa ne. To kawo yanzu dai, ba a sami wani sauyi ba a halin da ake ciki. Shugaba Obasanjo, har ila yau, bai iya ya shawo kan matsalar ba. Ko dai ya sa ido ababa na wakana, ko kuma ya tura dakaru yin ɗauki, inda sai tsananinsu ma ya fi na lokacin mulkin soji.

Ɗaya matsalar kuma, ita ce muhawarar da ake yi kan batun nan na ta zarce, inda shugaba Obasanjo ke nufin ci gaba da mulki duk da cewa, bisa ƙa’idojin kundin tsarin mulkin ƙasar a halin yanzu, ba shi da wannan damar. Shi dai Obasanjon, har ila yau, bai fito fili ya bayyana matsayinsa a kan wannan batun ba tukuna. Amma muƙarrabansa ne ke ta fafufutukar yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima, don manufar ta zarcen ta sami karɓuwa a cikinsa. A kan wannan batun ne rikici ya ɓarke a birnin Katsina, amma ba saboda zanen ɓatancin nan da ke ƙorafi a kansa ba.

To sai dai, a ko yaushe, akwai wasu `yan siyasa da dama, masu yin amfani da addini wajen neman cim ma burinsu. Ga irin waɗannan mara kishin ƙasarsu da makomarta kuwa, batun zanen ɓatancin nan ya zo ne kamar wani abin neman da ya samu.

Ƙona tutar ƙasar Denmark da majalisar jihar Kano ta yi a hukumance dai, ba wani kyakyawan misali ba ne ga jama’a, saboda wasu na iya ɗaukan hakan tamkar ba su dama ke nan ga afka wa waɗanda ke da ra’ayoyi daban da nasu.

Kamata ya yi dai shugabannin siyasa da na addinan ƙasar su gane cewa, matsalar Najeriya, a Najeriyan ce za a iya warware ta, amma ba a wani wuri daban ba, idan dai burinsu ne su samar wa ƙasar kyakyawar makoma. Ba za a iya cim ma wanna burin ba kuwa, sai an juya wa bambancin ƙabilanci da na addini baya, saboda Najeriya ƙasa ce mai al’ummai da al’adu daban-daban.

Abin farin ciki a nan dai shi ne, a Najeriyan ma, akwai wasu `yan tsiraru waɗanda suka fahimci cewa, haɗa kai wajen tsara wa ƙasar kyakyawar makoma cikin zaman lumana, shi ne abin da ya fi muhimmanci gare ta. A lal misali akwai kafofi kamar ƙungiyar nan ta „Muslin-Christian Dialog Forum“ ko kuma „Inter-Faith Mediation Center“ ta birni Kaduna, wadda saboda rawar ganin da ta taka wajen samad da zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban na ƙasar, ta yi ta samun lambobin yabo na gamayar ƙasa da ƙasa. Ko masu ta da zaune tsaye za su iya kwaikwayo da aikin da ´yan wannan ƙungiyar ke yi, su ma su canza ra’ayoyinsu ? Ko babu komai dai, za a iya cewa, mai yiwuwa sakamakon aikin da ƙungiyar ta yi a jihar ta Kaduna ne ya sa kawo yanzu ba a sami wani tashin hankali a nan ba.