Tashe-tashen hankulla a Afghanistan | Labarai | DW | 25.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe-tashen hankulla a Afghanistan

Ƙungiyar yan taliban a ƙasar Afghanistan ta kashe soja ɗaya na rundunar ƙasa da ƙasa.

Pierre Yves Sarzaud, ɗan kasar France, ya rasa ran sa, a cikin harin da mayaƙan taliban su ka abkawa wata rundunar ƙasar Afganistan da ya ke ba horo.

Sannan a ɗazunan ne, wani ɗan jaridar ƙasar Jamus, ya ƙetara rijiya da baya, bayan da yan taliban su ka sallamo shi, yan sa´a´o kaɗan bayan garkuwa da shi.

Yau ne kuma da dare,da kimanin ƙarhe 8 da rabi agogon GMT, wa´adin ƙarshe da yan taliban su ka bada ke kai ƙarshe a game da koreyawa nan 23 da su ka garkuwa da su.

Tunni dai yan taliban, sun bayana fille kan ɗaya daga cikin pirsinonin 23.

Sun yi barazanar kashe sauran 22, mudun fadar mulkinKabul, ba ta yi belin wasu mayaƙan taliban ba guda 8 da ke cikin hannun ta.