Tashe -tashen hankulla a ƙasar Irak | Labarai | DW | 25.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe -tashen hankulla a ƙasar Irak

Kamar yada a ka saba kullum, tashe tashen hankulla na ci gaba da hadasa assara rayuka a kasar Iraki,

A sahiyar yau, a kalla mutane 9 su ka rasa rayuka, a cikin hare hare daban-daban.

Sannan an kara gano gawwawakin wasu mutane 10, a gabacin birnin Bagadaza.

A nata bangare, rundunar Amurika, ta bayyana mutuwar wasu sojojin ta 2, a yankin Al Anbar da ke yamnmacin kasar.

Daga farkon yakin Iraki, zuwa yanzu, wannan su ne cikwan sijojin Amurika, na 2.323, da su ka sheka lahira a cikin hare haren kwatan bauna.

Shi kuwa, shugaban kasa, Jallal Talabani, a wani jawabi da ya gabatar, ya bayyana samun haske, a kikikakar, da a ke fama da ita, wajen girka gwamnati, watani 3 bayan zaben da aka gudanar.