1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankulla a ƙasar Irak

March 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bv61

Shugaban ƙasar Iraki, Jalal Talabani ya yi kira ga larabawa sunni da su daina kai hare hare ga rundunonin soja dake Irak.

A wani taron manema labarai da ya shirya a yau, Jallal Talabani, yayi huɗuba ga al´ummar Irak da cewar kai hare haren ga sojojin ƙasa da ƙasa ba hance da za ta sa a cimma burin da aka sa gaba ba.

Ya yi kiri wannan taron manema labarai, jim kaɗan bayan wata ganawa da yayi, da shugaban rundunar sojojin Amurika a Irak.

Saidai wannan kira ba shi ba ne na farko, da hukumomin Irak su ka bayi, amma har yanzu sun kasa dakatar ga hare haren.

A yau ma, yan ƙunar baƙin wake, sun kai hari, cikin tashar wani birni da ke kudu maso gabacin Bagadaza.

Mutane 7, sun rasa rayuka, a cikin wannan hari, wasu kuma kimanin10, sun ji mumunan raunuka.

Irak ,ta faɗa cikin wani saban bila´i, tun ƙarshen watan da ya gabata, a sakamakon harin da ya ruguza ɗaya, daga wuraren ibadar yan shi´a.

Hare haren ramuwar gayya, tsakanin yan sunna, da yan shi´a, ya zuwa yanzu, ya jawo mutuwar ɗaruruwan mutane daga ɓangarorin2.